in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Guterres ya zanta da zababben shugaban Amurka ta wayar tarho
2017-01-05 11:19:24 cri
A jiya ne sabon babban magatakardan MDD António Guterres ya zanta da zababben shugaban kasar Amurka Donald Trump ta wayar tarho, inda suka tattauna kan huldar dake tsakanin MDD da Amurka.

Mataimakin kakakin babban magatakardan Majalisar Dinkin Duniya Farhan Haq wanda ya bayyana hakan a taron manema labarai da aka yi jiya ya ce, jami'an biyu sun yi musanyar ra'ayoyi kan dangantakar MDD da Amurka, haka kuma Guterres ya bayyana fatansa na kara yin mu'amala tare da Trump bayan da aka rantsar da shi.

A ranar 1 ga watan Janairun bana ne António Guterres ya kama aikin sakatare-janar na MDD. A dayan bangaren kuma, za'a rantsar da Donald Trump a matsayin sabon shugaban Amurka a ranar 20 ga watan da muke ciki. A baya dai Trump ya bayyana ra'ayinsa a fili kan wasu muhimman batutuwa, ciki har da rawar da MDD ta taka, da Yarjejeniyar Paris da aka cimma game da magance matsalar sauyin yanayi, gami da kokarin da aka yi na wanzar da zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya, lamarin da ya janyo shakku da dama dangane da makomar alakar kasar Amurka da MDD.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China