Kwamandan rundunar Operation Lafiya Dole, Manjo.- Janar Lucky Irabor, ya shaidawa manema labarai a birnin Maiduguri cewa, an yi nasarar kama 'yan kunar bakin waken ne bisa rahoton sirri da suka samu.
Ya ce, sun kama 'yan kunar bakin wake, sai dai uku daga cikinsu sun tirje, inda suka yi kokarin kutsawa cikinsu, yana mai cewa basu da wata mafia da ta wuce bude musu wuta.
Manjo Janar Lucky Irabor ya kara da cewa, dakarun Nijeriya da takwarorinsu na Kamaru, na samun nasara a kokarin da suke na kwato yankunan da ke kusa da Kauyen Ngoshe da Dutsen Gwoza, inda ya ce yayin aikin, sun samu makamai da alburusai da dama.
Har ila yau, ya ce sun yi nasarar cafke wani daga cikin 'ya'yan kungiyar, mai lamba 164 cikin jerin 'ya'yan kungiyar da rundunar soji ta ayyana nemansu ruwa a jallo.
A wani labarin kuma, Manjo Janar Lucky Irabor ya tabbatar da batun kama shugaban Karamar Hukumar Mafa ta jihar Borno Shettima Lawal, wanda ake zargin na da alaka da kungiyar ta Boko Haram.( Fa'iza Mustapha)