Shugaban kasar ya ce, gano yarinyar ya kara kyautata fatan da ake da shi na wata rana za a kai ga gano sauran 'yan matan tare da sada su da iyalansu, kawaye da kuma al'ummominsu.
Ya kuma yabawa rundunar sojin kasar bisa dukufa da ta yi da binciken da ya kai ga gano Rakiya, yana mai bukatar dakarun su ci gaba da irin jajircewar da ya kai su ga fattatakar 'yan ta da kayar baya daga dajin Sambisa.
Buhari ya kuma tabbatar da kudurin gwamnatinsa, na ci gaba da taimakawa rundunar soji da duk abun da take da shi, wajen gano sauran 'yan matan tare da fattatakar matsalar ta'addanci a Najeriya.
Wannan al'amari na zuwa ne bayan an saki 'yan matan Chibok 21 a watan Oktoban da ya gabata, bayan an cimma yarjejeniya da wadanda suka sace su. ( Fa'iza Mustapha)