Mataimakin Shugaban kasar na musamman kan harkokin yada labarai, Malam Garba Shehu ne ya bayyana tabbaci cikin wata sanarwar da ya fitar, bayan wani al'amari da ya auku a fadar ranar Laraba, inda aka samu kuskuren sakin kunamar bindiga.
Ya ce al'amarin ya auku ne bayan bindigar pistol na wani da ya kai ziyara fadar, ya saki kuna bisa kuskure a lokacin da yake mika bindigar a bakin kofa kafin shiga fadar.
Mutumin wanda jami'in tsaro ne, ya kai ziyara fadar ne bisa gayyatar da aka masa, a matsayinsa na shaida kan wani bincike da ake gudanarwa. Jami'in dai ba ya cikin jami'an tsaro da aka girke a fadar Shugaban Kasar. ( Fa'iza Mustapha)