Wata sanarwar da kamfanin sarrafa albarkatun man kasar NNPC ya fitar a ranar Larabar nan, ta bayyana cewa, kwantiragin da gwamnati ta daddale da kamfanonin zai kammala ne bayan watanni 12.
Kazalika sanarwar ta ce, cikin wadannan kamfanoni, akwai na cikin kasar 18, da kuma na kasashen waje 11, da wasu matatun mai na waje 5. Sai kuma wasu kamfanonin mai na cikin kasar 3, da kuma sassan kasuwanci na kamfanin NNPC 2.
Da yake tsokaci yayin da zaman tantance sassan da suka nuna sha'awar shiga a dama da su a wannan harka, a ranar 26 ga watan Nuwambar bara, babban manajan daraktan kamfanin NNPC Maikanti Baru, ya baiwa al'ummar kasar tabbacin cewa, NNPC zai tsaya tsayin daka, wajen ganin an bi ka'idojin da doka ta tanada wajen zabar wadannan kamfanoni. (Saminu Hassan)