in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin za ta zamanantar da bangaren masana'antun kasar nan da shekarar 2020
2016-12-08 20:25:39 cri

Kasar Sin ta bayyana kudurinta na ci gaba da inganta sashen masana'antun kasar cikin shekaru biyar masu zuwa, a kokarin zamanantar da sashen na masana'antu tare da kara samar da sabbin dabarun ci gaba.

Wasu bayanai da mahukuntan kasar ta Sin suka fitar a yau, ya nuna cewa, ya zuwa shekarar 2020, za a zamanatar da muhimman sassan da masana'antun kasar suka saba amfani da su a baya.

Shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar da ma'aikatar kula da harkokin masana'natu da fasahar sadarwa ta zamani da ma'aikatar kudi suka fitar cikin hadin gwiwa, ya bayyana cewa, muddin aka zamanantar da bangaren masana'antun kasar, hakan zai taimaka wajen kara yawan kayayyakin da ake samarwa, rage kudaden da ake kashewa, rage yawan makashi da ake amfani da shi tare da bullo da sabbin dabarun ci gaba.

A cikin shekaru biyar masu zuwa, kasar Sin za ta gudanar da bincike tare da kara inganta na'urorin da za a rika amfani da su a masana'antun kasar, matakin da zai kara inganta harkokin masana'antu na zamani.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China