A cewar takardar bayanan, Sin za ta gudanar da karin bincike da kuma yin nazari game da wasu muhimman al'amurra da suka shafi fasaha, inda kuma za ta taho da samfuri daga duniyar Mars, da karamin tauraro, da Jupiter, da kuma duniyar tauraron.
Majalisar bayanan ta kara da cewa "idan an samu dama, za'a aiwatar da sakamakon binciken domin yin nazari da kuma samo amsa game da wasu muhimman batutuwan kimiyya kamar su gano takamamman asalin ita kanta duniyar wata, da sauran al'amurra da suka shafi yanayin rayuwa.
(Ahmad Fagam)