Takardar ta ce za a harba tauraron bincike na Chang'e-4, karkashin wani shiri da kasar ta tsara na shekaru 5, wanda ke da burin cimma nasarar binciken duniyar ta wata, da jigilar kayayyakin bincike daga duniyar watan bisa tsarin fasahar zamani mai zurfi.
Da fari dai ana sa ran harba kunbon Chang'e-5, wanda ake sa ran ya cika ka'idojin gwaji na kewaye, da sauka, tare da dawowa doron duniya a cikin shekara mai kamawa, gabanin sauran gwaje gwaje masu zurfi da za a gudanar bayan hakan.
Karkashin shirin, za kuma a gudanar da binciken yanayin doron duniyar wata, da sassan kasar ta, tare da gwaje gwajen kimiyya kan kayayyakin da za a gano a duniyar ta wata. (Saminu Hassan)