in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin za ta fara wani rangadi karo na 33 a yankin Antartic
2016-10-30 13:13:57 cri

Wani jirgin ruwan bincike na kasar Sin, mai ratsa kankara na Xuelong wato dragon dusar kankara, zai tashi a ranar Laraba daga Shanghai domin wani rangadin binciken kimiyya a yankin Antartic.

Sun Bo, mataimakin darektan cibiyar binciken yankunan sanyi na iyakacin duniya na kasar Sin, ya sanar a ranar Jumma'a da wannan sabon labari a yayin wani taron manema labarai. Wata tawagar dake kunshe da mambobi 256 za ta tashi a ranar 2 ga watan Nuwamba domin wani rangadi na kwanaki 161 kuma zai tafiyar tsawon kilomita dubu 31, a cewar mista Sun dake jagorantar wannan tawaga.

Za su kai ziyara a tashoshin Zhongshan, Kunlun, Taishan da Changcheng, kuma za su gudanar da wasu ayyukan bincike da dama. Tawagar za ta dawo Shanghai a ranar 11 ga watan Afrilun shekarar 2017.

Mista Sun ya gabatar da tafiyar a matsayin wani rangadin jaruntaka take wakiltar karfi da burin kasar wajen gudanar da ayyukan binciken duniya.

Jirgin ruwan binciken na Xuelong zai isa tashar Zhongshan dake yankin gabashin Antartic a farkon watan Disamba. Bayan sauke kayayyaki a cikin tashoshin Zhongshan, Kunlun da Taishan, jirgin ruwan zai samu karin kayayyaki a Chili. Zai yi binciken tekun Ross a karshen watan Janairu kana zai koma a tashar Zhongshan a karshen watan Fabrairu, kana zai tafi a farkon watan Maris domin dawo kasa.

Kasar Sin ta gudanar da rangadinta na farko a yankin Antartic a shekarar 1984 inda ta kafa tashohi guda hudu. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China