Wannan mataki na zuwa ne gabanin rantsar da shugaban kasar da aka zaba Nana Akufo Addo da za a yi a watan Janairun shekarar 2017.
Bisa kundin tsarin mulkin kasar ta Ghana dai shugaban kasar ne zai gabatar da sunayen mutane biyu da za a zaba a mukamin kakakin majalisa da kuma mataimakin kakakin majalisa na daya, yayin da ita kuma jam'iyyar NDC ta marasa rinjaye za ta zabi wanda zai rike mukamin mukaddashin kakakin majalisa.
Kwarya-kwaryar sakamakon zaben 'yan majalisun da aka fitar ya nuna cewa, jam'iyyar NPP ta lashe kujeru 170 yayin da NDC ta lashe 105. Gabanin zaben dai NDC ce ta ke kujeru 148 cikin 275 na majalisar. (Ibrahim Yaya)