in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Karancin kudin shiga daga bangaren man fetur ya sa Ghana ta rasa wani kaso da za ta yi amfani da shi wajen cike gibin kasafin kudi
2016-12-22 11:14:25 cri

Jiya Laraba, minista harkokin Kudi na kasar Ghana Seth Terkper, ya ce kasar, za ta yi asarar kashi biyar na kudin da ake bukata a shekarar kudi ta bana, sanadiyyar faduwar kudin shiga da take samu daga man fetur da kuma farashin musayar kudaden ketare.

Da yake ganawa da manema labarai, Ministan ya yi bayanin cewa, rashin samun tallafi daga gwamnatin na daya daga abubuwan da suka haifar da asarar.

Ya kuma alakanta wannan matsala da rashin aiwatar manufofin asusun bada lamuni na duniya IMF, da aka jinkirta domin yiwa dokar da ta kafa Babban Bankin Ghana garambawul, kamar yadda majalisar dokokin kasar ta nema.

A cewarsa, duk da matsalolin, kasar ta yi kokari wajen rike darajar takardar CEDI da kuma daidaita matsalar da aka samu na karancin iskar gas da ya yi mummunan tasiri a kan tattalin arzikinta.

Ya kara da cewa, sakamakon wannan al'amari, ana sa ran za a samu karin koma bayan sama da abun da aka yi hasashe da kashi daya da rabi zuwa kashi biyu. (Fa'iza)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China