Yanzu haka kasar Sin ta na amfani da kashi 40% na makamashin bola jari.
Rahoton ya yi nuni da cewa, an samu karuwar amfani da makamashin bola jari ne a sakamakon manufofin da kasashen Amurka da Sin da India da ma sauran wasu kasashe suke bullo da su da kuma raguwar kudin samar da wutar lantarki ta hanyar amfani da makamashin hasken rana da kuma iska. Matakan magance matsalar sauyin yanayi da gurbacewar iska da kuma bukatun nau'o'in makamashi suna daga cikin abubuwan da suke taimakawa ga bunkasuwar makamashin bola jari.(Lubabatu)