Shugaba Buhari wanda ya bayyana hakan cikin sakonsa na murnar shiga sabuwar shekara a jiya Lahadi, ya ce gwamnatinsa za ta kara kaimi wajen samar da guraben ayyukan yi, da yaki da cin hanci da rashawa, yana mai cewa nasarorin da gwamnatin tasa ta cimma ya zuwa wannan lokaci, sun karfafa masa gwiwa matuka.
Ya ce tuni aka fara sauya tsarin noma a sassan kasar daban daban, wanda hakan ya haifar da samun yabanya mai tarin yawa a shekarar 2016 da ta gabata, yayin da a hannu guda jahohin kasar ke da kokarin yin hadin gwiwa da sauran masu ruwa da tsaki wajen bunkasa noman shinkafa.
Shugaba Buhari ya kara da cewa lokacin dogaro kan albarkatun mai domin samun kudaden musaya na ketare na gushewa, kuma nan gaba kadan cikin wannan shekara, al'ummar Najeriya za su kara amfana daga nasarorin da gwamnatinsa ke samu a fannonin raya kasa daban daban.
Kaza lika ya yi kira ga 'yan Najeriya da su hada kai da juna, yana mai tabbatar da cewa wahalhalun da ake fama da su yanzu haka na daf da zama tarihi. (Saminu Hassan)