in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
NSCDC ta girke jami'an tsaro gabanin bukukuwan sabuwar shekara
2016-12-31 14:05:00 cri

Hukumar tsaron rayukan al'umma da aka fi sani da civil defence a Najeriya, ta tura jami'anta sama da dubu 40 a muhimman wurare a fadin kasar domin tabbatar da tsaro a lokacin bukukuwan sabuwar shekarar ta 2017.

Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar Emmanuel Okeh ya rabawa manema labarai a jiya Juma'a a Abuja, ya ce jami'an za su sa ido sosai domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama'a, da kuma tabbatar da ganin an gudanar da bukukuwan sabuwar shekarar lami lafiya.

Ya ce daga cikin shirin tabbatar da tsaron, za'a yi amfani da kwararrun karnuka wadanda suka kware wajen yaki da ta'addanci, da tawagar jami'ai na musamman, da jami'an bada agajin gaggawa da kuma motocin daukar marasa lafiya.

Ya ce za'a rarraba jami'an ne zuwa wasu muhimman wurare da suka hada da manyan titunan mota, da filayen jirgin sama, da wuraren ibadu, da wuraren shakatawa da dai sauransu.

Ya kara da cewa, babban kwamandan hukumar ta NSCDC na kasa, ya bada umarnin tura jami'ai kimanin 2,700 zuwa yankin arewa maso gabashin kasar, baya ga jami'ai 2,300 da aka tura tun da farko zuwa yankunana da aka kwato su, da kuma sansanonin 'yan gudun hijira domin tabbatar da tsaron rayukan mazauna yankunan.

Kwamadan ya gargadi kwamandojin hukumar na jahohi, da su tura jami'an dukkan yankunan da ake da fargabar fuskantar harin 'yan ta'adda, da masu cutar da jama'a.

Kana ya baiwa jami'an sojoji da sauran hukumomin tsaron Najeriya tabbacin yin aiki tare wajen samar da muhimman bayanai da kuma aikin sintiri domin tabbatar da tsaro a kasar baki daya.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China