in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kakakin ma'aikatar kasuwanci ta kasar Sin ya mai da martani kan batun sayen kamfanoni da kamfanonin Sin suke yi a ketare
2016-04-20 11:27:51 cri
A jiya Talata 19 ga wata, kakakin ma'aikatar kasuwanci ta Sin, Shen Danyang ya mai da martani kan ra'ayin wasu kasashe da kafofin yada labarai na ketare cewa, wai kamfanonin Sin suna kokarin sayen sauran kamfanonin ketare domin mallakar sassa daban daban na duniya, inda Shen ya furta cewa, hakan ya faru ne a sakamakon alkaluman da wasu hukumomin kididdiga suka bayar da ba na daidai ba, da kuma yunkurin wasu kafofin yada labarai na jawo hankulan kowa da kowa, kamata ya yi a dauki batun yadda ya kamata.

A kwanan baya, wasu kafofin yada labarai sun bayyana cewa, a farkon watanni uku na bana, jimillar kudin da kamfanonin Sin suka kashe domin sayen sauran kamfanoni a ketare ya kai dala biliyan 113, a yunkurin mallakar duniya. Har ma wasu kasashe sun gabatar da dokoki irin na nuna bambanci ga kamfanonin Sin a jere.

Game da wannan batu, a gun taron manema labaru da ma'aikatar kasuwanci ta Sin ta shirya, Shen Danyang ya bayyana cewa, bisa alkaluman da ma'aikatar ta bayar, an ce, a farkon watanni uku na bana, jimillar kudin da kamfanonin Sin suka kashe domin sayen sauran kamfanoni a ketare ya kai dala biliyan 16.56 kawai, wanda ya sha bamban sosai da alkaluman da wasu kafofin yada labarai suka bayar.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China