in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin Sin ta fidda takardar bayani a kan tsarin tauraron dan Adam dake ba da jagoranci kan zirga-zirga na Beidou
2016-06-16 11:25:18 cri

Yau Alhamis 16 ga wata, ofishin watsa labarai na majalisar gudanarwar kasa ta Sin ya samar da takardar bayani a kan tsarin tauraron dan Adam dake ba da jagoranci kan zirga-zirga na Beidou, inda ya bayyana cewa, tsarin Beidou tsarin taurarin dan Adam ne mai zaman kansa da kasar Sin ta samar don kare tsaron kasar da kuma raya tattalin arziki, kana, tsarin ya kasance wani muhimmin aiki da kasar Sin ke gudanarwa a sararin samaniya wajen samar wa masu yin amfani da tsari na kasa da kasa taimakon zirga-zirga ko da yaushe.

Takardar ta ce, bisa bunkasuwar tsarin Beidou da wasu ayyukan dake shafar wannan tsari, an riga an fara yin amfani da tsarin a fannin sufuri, aikin su, hasashen yanayi, labarin kasa, yin rigakafi kan gobarar daji, ayyukan wutar lantarki, da aikin ceto da dai sauransu, a nan gaba kuma, za a ci gaba da yin amfani da tsarin a fannoni daban daban dake shafar zaman rayuwar al'ummomin kasa da kasa na yau da kullum, domin ba da sabbin gudummawa ga bunkasuwar tattalin arziki da zaman takewar al'ummar kasa da kasa.

Haka zalika, an ce, tsarin tauraron dan Adam dake ba da jagoranci kan zirga-zirga zai amfana wa dukkanin kasashen duniya, shi ya sa, kasar Sin tana son ciyar da hadin gwiwar kasa da kasa gaba cikin himma da kwazo ta wannan fanni. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China