in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin: An dawo da wadanda ake nema kimaninsu 158 daga kasashen ketare
2017-01-05 20:43:50 cri

Daga watan Satumbar shekarar 2014 ya zuwa wannan lokaci, hukumar SPP ta kasar Sin, wadda ke bin bahasin wadanda suka aikata laifuka suka kuma tsere daga kasar, ta tiso keyar irin wadannan masu laifi har su 158 daga kasashen duniya daban daban.

Da yake karin haske game da hakan, daya daga kusoshin hukumar ta SPP Wan Chun, ya ce ana bincike kan kudi da kadarori da yawansu ya kai Yuan biliyan 1.73, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 251.4, wadanda ke da alaka da laifukan da ake zargin mutanen da aikatawa.

Hukumar SPP dai ta kaddamar da shiri na musamman, domin farautar masu tafka almundahana su kuma tsere kasashen ketare. Ya ce, tsakanin watan Janairu zuwa Nuwambar da ya shude, SPP ta dawo da mutane 41 daga kasashe da yankuna 18, an kuma kwato kudade da kadarori da darajarsu ta kai Yuan miliyan 516.

Mr. Wan ya ce, cikin irin wadannan mutane da ake zargi tuni aka yanke wa 40 hukunci, yayin da wasu kuma 7 ke fuskantar shari'a a kotu.

Kasar Sin dai ta rattaba hannu kan wasu yarjeniyoyi 54 masu alaka da hadin gwiwa a fannin shari'a, da wasu 41 da suka shafi neman damar tiso keyar 'yan kasar da ake zargi da tserewa daga kasar bayan aikata laifuka. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China