in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Haramcin cinikin hauren giwa na kasar Sin ya baiwa kasa da kasa kwarin-gwiwa
2017-01-05 13:56:02 cri
Kwanakin baya, shugaban hukumar kare namun daji ta kasar Kenya ya bayyana cewa, kasar Sin za ta dakatar da duk wani aiki na sarrafawa da cinikin hauren giwa gami da kayan dake da nasaba da shi, lamarin dake da matukar muhimmanci ga yaki da aika-aikar farautar giwaye da haramtaccen cinikinsu a duk duniya.

A cewar jami'in na Kenya, kamata yayi sauran kasashe su yi koyi da kasar Sin.

Shugaban hukumar kula da harkokin namun daji ta Kenya da ya zanta da kamfanin dillancin labarai na kasar Sin wato Xinhua, ya ce, farautar giwaye da sauyin yanayi, muhimman dalilai ne da suka jawo raguwar adadin giwaye a duniya, sai dai haramcin da gwamnatin kasar Sin ke aiwatarwa na cinikin hauren giwa, zai ba kasashe daban-daban kwarin-gwiwar hada kai domin yaki da ayyukan farautar giwayen, tare da kara fadakar da jama'a kan muhimmancin kare namun daji.

A cewar wannan jami'i, hana cinikin hauren giwa da kasar Sin ta yi, ya na da muhimmanci matuka wajen farfado da shirin kare namun daji na kasar Kenya da ma sauran wasu kasashen Afirka, al'amarin da ya haifar da wani sabon kuzari na kare giwaye bisa doka da oda. 'Kwararan matakan da gwamnatin kasar Sin ke dauka za su kawo karshen haramtaccen cinikin hauren giwa a duniya, ina fatan sauran kasashe za su yi koyi da kasar Sin', in ji wannan jami'i na Kenya.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China