Cikin sanarwar da mista Ban Ki-moon ya fitar, ya yabawa jama'ar kasar Gambia kan yadda suka gudanar da zaben na wannan karo yadda ya kamata, wato a ranar 1 ga watan Disamban da muke ciki, sannan ya taya Adama Barrow murnar lashe zaben shugabancin kasar da aka gudanar. Ban da wannan kuma, babban sakataren ya jinjina wa shugaba mai ci Yahya Jammeh, kan yadda ya nuna halin dattaku tare da taya abokin takararsa murna samu nasara a zaben. A cewar Ban Ki-moon, MDD tana son ci gaba da rufawa jama'ar kasar Gambia baya, kan kokarinsu na tabbatar da hakkin dan Adam, da neman samun ci gaba mai dorewa.
A jiya Jumma'a ne hukumar zaben kasar Gambia ta sanar da cewa Adama Barrow ne ya lashe zaben da aka gudanar da ranar 1 ga watan Disamba bayan da ya samu yawan kuri'u fiye da kashi 45 cikin 100, inda hakan ya bashi damar zama sabon zababben shugaban kasar Gambia.(Bello Wang)