in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
kasashen Sin da Gambia sun farfado da huldar diplomasiyya a tsakaninsu
2016-03-17 19:19:22 cri

Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi da takwaransa na kasar Gambiya Neneh Macdouall-Gaye sun rattaba hyannu a kan sanarwar hadin gwiwwa a ranar Alhamis din nan, inda suka sanar da farfado da huldar diplomasiyya a tsakanin kasashen biyu.

Sanarwa ta bayyana cewa gwamnatin jama'ar kasar Sin da gwamnatin Jamhuriyar Islama ta Gambiya, a bisa ga bukatar da ra'ayin al'ummar kasashensu, na son inganta da karfafa dangantaka na abota da hadin gwiwa na kasashen biyu da kuma amfanar jama'ar su baki daya, kuma bisa sharuddan MDD da dokokin kasa da kasa, sun amince sun kuma yi shawarar farfado da huldar diplomasiya na Jakadu daga wannan rana da aka rattaba hannu a kan sanarwar.

Gwamnatin Gambiya ta kuma amince cewa Sin guda daya ce a duniya kuma gwamnatin al'ummar kasar Sin ce kadai ke da ikon wakiltar jama'ar ta baki daya, sannan kuma Taiwan tana karkashin ikon kasar ta Sin, inji sanarwar.

A lokacin tattaunawar da ke tsakanin ministocin harkokin wajen kasashen biyu tun da farko a ranar Alhamis din, Mr. Wang Yi ya bayyana farfado da huldar diplomasiya tsakanin kasashen biyu a matsayin wani abin tarihi da kuma burin al'ummar kasashen biyu.

Ya ce, al'ummar kasar Sin a ko da yaushe tana daukar al'ummar Gambiya da zuciyar abotan arziki, sannan farfado da huldar diplomasiya a matakin jakada ya sake bayyana yadda kasashen biyu ke nufin juna da alheri.

Mr. Wang Yi ya ce, kasar Sin a shirye take ta inganta dangantakar mutunta juna, ta fadada hadin gwiwa, ta kuma kara musanyar jama'ar ta tsakanin ta da Gambiya, sanna kuma za ta goyi bayan kasar a kokarin ta na taka muhimmiyar rawa a fagen duniya da sha'anin shiyya- shiyya.(Fatimah Jibril)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China