Cikin sakonsa na taya murnar, shugaban kasar Sin ya ce tun bayan da kasashen Sin da Gambia suka maido da hulda a tsakaninsu a watan Maris na bana, bangarorin biyu suke kokarin aiwatar da ayyukan hadin kai a tsakaninsu, ayyukan da suke da makoma mai haske. Hakan, a cewar shugaban kasar Sin, ya kasance shaidar cewar, yadda aka maido da hulda tsakanin kasashen 2 ya dace da moriyar jama'ar kasashen 2.(Bello Wang)