in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya ya jaddada yin kiran mika mulki cikin ruwan sanyi a Gambia
2016-12-23 09:50:39 cri
A jiya Alhamis ne, kakakin Majalisar Dinkin Duniya ya ce Sakatare Janar na Majalisar, Ban Ki-moon, ya jaddada kira ga shugaban kasar Gambia Yahya Jammeh, da ya mika mulki ga zababben shugaban kasar cikin ruwan sanyi ta hanyar da ta dace.

Farhan Haq, mataimakin kakakin Majalisar, ya ce Ban Ki-moon, ya yi kiran ne lokacin da yake tattaunawa game da rikicin siyasar kasar, da wakilin kasar Gambia na dindindin a majalisar, dake shirin barin gado Mamadou Tangara.

Kakakin na Majlisar Dinkin Duniya ya kara da cewa, Sakatare Janar din ya yabawa Jakada Mamadou Tangara tare da wasu jam'ian diflomasiyyar kasar 10, bisa kiran da su ka yiwa shugaba Jammeh, da ya shirya mika mulki cikin ruwan sanyi ga zababben shugaban kasar Adama Barrow.

Ban Ki-moon ya kuma bayyana damuwa game da kin mika mulki da Shugaba Jammeh ya yi kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanada, duk da irin kiraye-kirayen da shugabannin kasashen duniya ke masa na mika mulkin.

Sakatare Janar din ya kuma jaddada kudurin Majalisar Dinkin Duniya na goyon bayan mika mulki a kan lokaci cikin ruwan sanyi, kamar yadda al'ummar kasar ke muradi.

A ranar 9 ga watan nan na Decemba ne shugaban kasar Gambia Yahya Jammeh ya bayyana kin amincewarsa da sakamakon zaben da aka yi ranar 1 ga watanan nan, inda ya yi kira ga al'ummar kasar su kara yin zabe, mako daya ke nan bayan ya amince da kayen da ya sha.

Da farko, da yake jawabi ga al'ummarsa ta gidan talabijin na kasar, a ranar 2 ga watan nan na Decemba, Shugaba Jammeh ya amince da kayen da ya sha har ma ya taya zababben shugaban kasar murna.

Yahya Jammeh dai, ya kasance a kan karagar mulkin kasar tun a shekarar 1994.(Fa'iza)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China