in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sakatare janar na MDD ya taya Akufo-Addo murnar lashe zaben shugaban kasar Ghana
2016-12-10 17:55:21 cri

Babban magatakardan MDD Ban Ki-moon, ya taya Nana Akufo-Addo murnar lashe zaben shugaban kasar Ghana.

A wata sanarwa da mai magana da yawaunsa ya fitar, Ban ya kuma yabawa shugaban kasar ta Ghana mai barin gado John Dramani Mahama bisa irin juriyar da ya nuna na amincewa da shan kaye a zaben, da kuma tabbatar da zaman lafiya a lokacin zaben a duk fadin kasar.

Sanarwar ta ce mista Ban Ki-moon, ya jaddada aniyar MDD wajen tallafawa gwamnatin kasar Ghana wajen tabbatar da dorewar mulkin demokaradiyya da cigaban kasa.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ga Wasu
v Akufo-Addo ya lashe zaben shugaban kasar Ghana 2016-12-10 13:20:38
v An fara babban zabe a kasar Ghana 2016-12-07 19:21:38
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China