in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An fara babban zabe a kasar Ghana
2016-12-07 19:21:38 cri

A yau Laraba da misalin karfe 7 na safe agogon kasar Ghana ne sama da mutane miliyan 15 da aka yiwa rijista za su kada kuri'unsu a rumfunan zabe kimanin 29,000 a sassa daban-daban na kasar.

Dan takarar jam'iyyar NDC kana shugaba kasar mai ci John Dramana Mahama, yana neman wa'adi na biyu na shekaru 4 a zaben na yau. Nana Akufo-Addo, shugaban jam'iyyar adawa NPP shi ne babban mai kalubalantar sa a zaben.

Mahama dai yana da farin jini a wajen al'ummar kasar ta Ghana, sai dai ana zarginsa da rashin daukar matakan da suka dace kan tafiyar hawainiyar da tattalin arzikin kasar ke fuskanta, rashin aikin yi, hauhawar farashin kaya a lokacin wa'adin farko na mulkinsa.

Haka kuma, a yau ne za a zabi 'yan majalisun dokoki 275 bisa wa'adin shekaru 4. Ana sa ran rufe rumfunan zabe da karfe 5 na yamma agogon Ghana. A ranar Jumma'a ne za a sa ran da sakamakon zaben.( Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China