in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Akufo-Addo ya lashe zaben shugaban kasar Ghana
2016-12-10 13:20:38 cri

Hukumar zaben kasar Ghana ta sanar da sakamakon zaben shugaban kasar a jiya Jumma'a, dan takarar jam'iyyar adawa ta New Patriotic Party Nana Akufo-Addo ne ya lashe zaben, kuma shi ne zai zama sabon shugaban kasar.

Hukumar zaben kasar ta Ghana ta bayyana cewa, Akufo-Addo ya samu kuri'u fiye da miliyan 6 da dubu 700 daga cikin runfunan jefa kuri'u 271 da aka yiwa rajista a dukkan kasar, inda ya samu kashi 53.85 cikin 100 na dukkan kuri'un da aka jefa. Dan takarar jam'iyyar National Democratic Congress kuma shugaban kasar mai ci John Mahama ya samu kuri'u kimani miliyan 4 da dubu 700, wanda ya kai kashi 44.4 cikin 100.

Sai dai har yanzu ba a sanar da sakamakon zaben majalisar dokokin kasar ba. Bisa kididdigar da aka yi, yawan mutane da suka jefa kuri'un zaben ya zarce miliyan 10, wanda ya kai kashi 68.6 cikin dari bisa na yawan mutanen da suka yi rajistar zabe a duk fadin kasar.

A ranar Larabar da ta gabata ne aka gudanar da zaben shugaban kasar ta Ghana, 'yan takarar shugabancin kasar 7 ne suka fafata a zaben. Bisa kundin tsarin mulkin kasar Ghana, wa'adin shugabancin kasar shekaru 4 ne. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China