Wata sanarwa da kakakin sojojin Najeriyar Kanar Sani Usman ya rabawa manema labarai a yau Jumma'a, ya ce, sun kalli faifan bidiyon wanda jagoran kungiyar Abubakar Shekau ya fito yana wasu kalamai marasa tsuhe,kuma an dauki shi ne a wani wuri da ba a bayyana ba.
Abubakar Shekau dai ya fito a cikin bidiyon yanan karyata cewa, kungiyar tana nan daram a tungarta da ke dajin Sambisa
Sai dai kuma rundunar sojojin Najeriyar tana nanata cewa, ta kwace maboyar karshe ta makayan kungiyar da ke Dajin na Sambisa. Yanzu dai ana ci gaba da tantance sahihancin faifan bidiyon da kungiyar Boko Haram din ta fitar.(Ibrahim)