Ministan yada labaru da raya al'adu na kasar Lai Mohammed, shi ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa, inda ya ce wasu manyan jami'an gwamnatin za su halarci bikin bude hanyoyin, wato hanyar Maiduguri zuwa Gubio zuwa Damasak, da kuma hanyar Maiduguri zuwa Mungono zuwa Baga.
Da farko dai an rufe manyan hanyoyin mota biyu ne, sakamakon matsalar hare haren mayakan Boko Haram a yankunan, hanyoyin na da matukar tasiri ga ci gaban tattalin arikin tafkin Chadi
A ranar Larabar da ta gabata ne shugaban Najeriyar Muhammadu Buhari, ya sanar da cewa sojojin kasar a shiyyar arewa maso gabas, sun yi nasarar fatattakar Boko Haram daga dajin Sambisa, wanda shi ne kadai ya rage a matsayin mafaka ga mayakan na Boko Haram.
Dajin na Sambisa, wanda ke kunshe da tsaunuka a yankin Gwoza kusa da kan iyakar jamhuriyar Kamaru, ya kasance a matsayin sansanin da mayakan 'yan ta'adan ke amfani da shi kafin dakarun Najeriya su tarwatsasu.
Boko Haram tana yunkurin aiwatar da shari'ar musulunci ne a arewacin Najeriya, kasar da ta fi yawan al'umma a nahiyar Afrka, kana kasa mafi arzikin danyen mai a nahiyar Afrika. (Ahamd Fagam)