Trump ya bayyana shi a matsayin kwarraren masananin harkokin kasuwanci na duniya, kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Twitter.
Ya ce babban abin da yafi birge shi game da Rex Tillerson shi ne, yana da matukar kwarewa wajen tafiyar da al'amurran hulda da gwamnatocin kasashen waje, kamar yadda mista Trump ya wallafa a shafin nasa na twitter.
Tillerson, mai shekaru 64, wanda ke rike da matsayin shugaban gudanarwar kamfanin man dake jahar Texas tun a shekarar 2006. Kamar dai yadda mista Trump yake, shi kansa Tillerson bashi da wata kwarewa game da sha'anin gudanar da gwamnati, kuma kawo yanzu ba shi da wata masaniya game da batun hulda da kasashen duniya.
Jaridar Wall Street Journal ta rawaito wata majiya na cewa, sanarwar da aka gabatar na ayyana sunan babban jami'in kamfanin man na Exxon Tillerson a wannan mukami ta baiwa manyan jami'an kamfanin Exxon mamaki, ciki har da shi kansa mista Tillerson din.
To sai dai kasancewar Tillerson, fitaccen masanin harkokin kasuwanci ne, zai iya yin amfani da kwarewarsa wajen tafiyar da harkokin diplomasiyyar, kamar yadda jaridar ta wallafa.
Babban jami'in kamfanin na Exxon, Tillerson, wanda ya shirya ajiye aikinsa a kamfanin man wanda ke ma'amala da kasashe sama da 50, yana da kyakkyawar dangantaka da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin tun a shekarun 1990.
Tillerson, wanda kasar Rasha ta taba baiwa lambar yabo ta abokin mu'amala a shekarar 2013, saboda da irin kyakkyawar dangantakar dake tsakaninsa da kasar Rasha.
Shi dai mista Tillerson ya fara aiki ne da kamfanin na Exxon ne tun a shekarar 1975, kuma kare mafi yawan rayuwarsa ne a aikin kamfanin.(Ahmad Fagam)