Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya ja hankalin kasashen kungiyar BRICS, da su kara azama wajen tabbatar da zaman lafiya da ci gaban daukacin sassan duniya bai daya.
Mr. Wang wanda ya yi wannan tsokaci, yayin taron ministocin harkokin waje na kungiyar ta BRICS, a wani bangare na babban taron MDD dake gudana a birnin New York, ya ce kwazon kasashen kungiyar ta BRICS a baya bayan nan, ya taikamawa yunkurin da ake yi na warware rikicin kasar Syria ta hanyar siyasa.
Kaza lika ya jinjinawa kasashe mambobin kungiyar ta BRICS, bisa tallafin su na tabbatar da nasarar taron kolin kungiyar G20 da ya gudana 'yan kwanakin baya a birnin Hangzhou, taron da ya zamo ginshiki na tunkarar harkokin ci gaban tattalin arzikin duniya baki daya.
Mr. Wang ya kara da cewa, taron na G20 ya amince da ajandar wanzar da ci gaba mai dorewa nan da shekara ta 2030, manufar dake kunshe da bunkasa masan'antu a nahiyar Afirka, da ma sauran kasashen dake sahun baya a fannin ci gaba.
Daga nan sai ya yi kira ga kasashe mambobin kungiyar ta BRICS, da su zaburar da kasashe mafiya ci gaba, wajen cika alkawarun da suka dauka ga kasashe masu tasowa. Ya ce kamata yayi tsarin jagorancin duniya ya dace da halin da ake bukata, game da sauyin siyasa da tattalin arzikin duniya. Har wa yau ya jaddada muhimmnacin samar da wakilci da zai game daukkanin sassan duniya, tare da baiwa kasashe manya da kanana dama ta fada-a-ji, wadda za ta dace da cimma nasarar kudurorin ci gaban duniya.