in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Congo ya nuna yabo kan ci gaban mamaki na kasar Sin
2016-07-07 09:58:57 cri
Shugaban kasar Congo, Denis Sassou-Nguesso, ya nuna yabo a ranar Laraba kan ci gaban kasar Sin, da hasashen yawan manyan damammaki ga kasarsa tare da taimakon huldar dangantaka.

Mista Sassou-Nguesso, wanda ya kawo ziyararsa ta farko a kasar Sin a shekarar 1980, ya kuma kawo rangadi gomai a wannan kasa. Ya yi kuma la'akari da idonsa sauye sauyen da kasar Sin ta samu tun lokacin kaddamar da manufar yin gyare gyare cikin gida da bude kofa ga kasashen duniya, tare da kimanta wadannan sauye sauye na abin "mamaki matuka"

Da yake daukar misali kan Shenzhen, shugaban Congo ya bayyana a yayin wata hira da kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, wannan birnin na kudancin Sin na kunshe a halin yanzu da manyan masana'antu na zamani, idan aka duba a shekarun baya kan matsayinsa na wani karamin kauyen masunta. A cewarsa, huldar dangantaka tsakanin kasarsa da Sin ta kara habaka da karfi. Tun lokacin maido da huldar diplomasiyya a shekarar 1964, kasashen biyu sun yi aiki tare a fannonin da suka hada da kiwon lafiya, saka, ababen more rayuwa, sufuri, bangaren tashoshin ruwa, makamashi da sadarwa.

Shugaban kasar Sin, Xi Jinping, da mista Sassou-Nguesso sun yi wata ganawa a ranar Talata a nan birnin Beijing, tare da yin alkawari bisa wannan dama da ta samu domin kara daga huldar dangantakarsu a wani sabon matsayi na huldar dangantaka ta moriyar juna daga dukkan fannoni. Kasar Congo, a cewar mista Sassou-Nguesso, tana jiran karin hadin gwiwa tare da kasar Sin a fannoni da dama, da ya hada da bunkasa karfin masana'antu wajen sarrafa kayayyaki. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China