Shugaban na Sudan ya kuma yi kira ga dukkan bangarori da suka yi watsi da shirin sasantawa na kasar, da su martaba kundin da taron sasantawa na kasar ya amince da shi a watan Oktoban da ya gabata. Ya kuma nanata goyon bayan kasar na samar da zaman lafiya a Sudan ta kudu tare da ganin an aiwatar da dukkan yarjejeniyoyin da kasashen biyu suka sanyawa hannu.
Al-Bashir ya ce, kundin ya shafi kowa da kowa kuma muryar al'ummar Sudan ce, kana kofa a bude take ga duk wadanda suka yi watsi da shirin a baya. (Ibrahim)