in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sudan ta ki shigowar tallafin jin-kai da ba'a tantance shi ba cikin kasar
2016-12-29 13:37:09 cri
Jiya Laraba, Gwamnatin kasar Sudan ta sake nanata cewar, ba ta yarda da shigar da duk wani tallafin jin-kai da ba'a tantance ba cikin kasar, musamman zuwa wasu yankunan dake fama da fadace-fadace, ciki har da jihohin Kordofan ta Kudu da Blue Nile.

Shugaban kwamitin kula da harkokin agajin jin-kai na kasar Sudan Ahmed Mohamed Adam ya ce gwamnati ba ta taba yarda da shigar tallafin jin-kai da ba a tantance ba cikin kasar, inda ta ki kai kayan tallafin jin-kai da ba a amince da su ba ga yankunan da suke fama da yake-yake.

Ahmed Adam ya jaddada cewa, gwamnati ba zata ja da baya ba a kan wasu muhimman batutuwa, lokacin da take shawarwari da kungiyoyi masu adawa da ita.

Tuni rahoto daga kafofin watsa labaran kasar Sudan ya ce, gwamnatin Sudan da kungiyar 'yan adawa mai suna SPLM-N sun cimma daidaito, inda gwamnati ta yarda da shigar da kashi 20 bisa dari tallafin jin-kai zuwa na yankunan dake karkashin ikon kungiyar SPLM-N ta kasar Habasha. Amma kungiyar SPLM-N ta musunta wannan labarin.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China