Ministan man fetur da iskar gas na kasar Sudan Muhammad Zayed Awad, ya ce tun asali, yarjejeniyar ta shekaru uku ce, kuma a yanzu sun kara tsawaita ta zuwa wasu shekaru uku.
Ya yi bayanin cewa, kudin fitar da man Sudan ta Kudu ta iyakokin Sudan, zai ci gaba da kasancewa yadda yake, wato dala ashirin kan kowace gangar mai
Yayin da takwaransa na kasar Sudan ta Kudu, Ezekiel Gatkuoth a nasa bangare, ya bayyana jin dadi kan kara tsawaita yarjejeniyar da kasashen biyu suka cimma.
Ya kuma jadadda kudurin kasarsa na aiwatar da dukkan kunshin yarjejeniyar, yana mai cewa kasashen biyu sun amince su hada hannu kan batutuwan da suka shafi man fetur, tare da amfani da cibiyar horar da ma'aikatan mai wajen ba da horo, aiwaratar da bincike da kuma gwaje-gwaje.
Yarjejeniyar da kasar Sudan da Sudan ta Kudu suka cimma a watan Satumban 2012, ya yi tanadin cewa, Juba za ta bada dala biliyan uku ga Sudan a matsayin tallafi cikin shekaru uku, baya ga haka, gwamnatin Sudan ta Kudu za ta rika biyan kudin fitar da mai na dala ashirin kan kowace ganga. (Fa'iza)