in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashen Sudan da Habasha sun amince da samar da sabbin dabarun da za su fadada dangantakarsu
2016-12-27 09:44:58 cri
A jiya Litinin ne, kasar Sudan da takwararta ta Habasha, suka amince da samar da sabbin dabarun da za su bunkasa dangantakarsu, tare da ci gaba da tuntubar juna da kuma hada hannu wajen magance batutuwan da suka shafe su.

Ministan harkokin wajen Habasha Workneh Gebeyehu, ya jinjinawa dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, yana mai bayyana shi a matsayin abun koyi, inda ya lashi takobin kara fadada shi domin kara cin gajiyarsa.

Ya kara da cewa, kasashen biyu sun amince da samar da wani tsari na din din din, ta yadda za su rika musayar bayanai.

A nasa bangaren, wani mataimakin shugaban kasar Sudan, Ibrahim Mahmud Hamid, ya tabbatar da kudurin gwamnatin kasarsa, na ci gaba da kokarin samar da dabarun da za su inganta dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.

Ministan harkokin wajen Habasha dai ya isa birnin Khartoum na Sudan ne a ranar Lahadi, domin tattaunawa kan batutuwa da suka shafi kasashen Sudan da Habasha. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China