Jami'an 'yan sanda a Najeriya, kasa mafi yawan al'umma a nahiyar Afrika, sun tsaurara matakan tsaro a duk fadin kasar, domin nasarar gudanar da bukukuwan kirsimeti da na sabuwar shekara.
Mai magana da yawun hunkumar 'yan sandan kasar Don Awunah, ya bayyana cikin wata sanarwa da aka baiwa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, jami'an 'yan sandan kasar sun shirya dabarun tabbatar da tsaro, domin ganin an kammala bukukuwan kirsimetin lami lafiya a duk fadin kasar.
Ya ce tuni babban sifeton 'yan sandan kasar Ibrahim Idris, ya tura jami'an zuwa wasu muhimman wurare a kasar domin samar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama'ar kasar a lokacin bukukuwan kirsimetin.
A cewarsa, an baza jami'an a kan manyan titunan motan kasar da wuraren ibadu, da kuma wuraren shakatawa domin gudanar da sintiri har zuwa lokacin kammala bukukuwan.
Kakakin 'yan sandan ya kuma gargadi masu lura da wuraren taruwar jama'a, da su sa ido sosai ga irin mutanen dake zirga zirga a wuraren a lokutan bukukuwan.
Sannan ya bukaci jama'a su gaggauta sanar da hukumomi da zarar suka ga bakuwar fuska da ba su amince da ita ba.
Bugu da kari Awunah, ya jaddada haramcin yin amfani da abubuwan fashewa na wasan wuta a kasar.(Ahmad Fagam)