in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Minista: Najeriya za ta hanzarta kammala aikin layin dogo na Legas zuwa Calabar
2016-12-25 13:20:52 cri

Ministan sufuri na Najeriya ya ce gwamnatin tarayya za ta kammala ayyukan gyaran tsoffin layukan dogo, da kuma kammala aiki gina layin dogo wanda ya tashi daga Legas zuwa Calabar.

A wata sanarwa da ya baiwa kamfanin dillancin labarai na Xinhua jiya Asabar, ministan sufurin Najeriya Rotimi Amaechi, ya ce, ana sa ran kammala aikin gyaran layin dogo daga Itakpe zuwa Ajaokuta zuwa Warri, da kuma aikin gina layin dogo daga Legas zuwa Calabar cikin lokacin da aka ware don gudanar da ayyukan.

A cewarsa, gwamnatin kasar za ta tabbatar da kammala aikin layin dogo daga Kano zuwa Legas domin saukaka zirga zirgar mutanen da kuma kayayyaki.

Ya ce za'a fara aikin layin dogo daga Legas zuwa Ibadan a watan Janairun shekarar 2017 mai kamawa.

Ministan sufurin ya ce, gwamnatin shugaba Muhammad Buhari, ta damu matuka wajen ganin an farfado da tattalin arzikin kasar.

Amaechi ya ce babban burin da wannan gwamnatin tasa a gabanta shi ne, yadda za ta biya muradun al'ummar kasar, ya kara da cewa, gwamnatin tana kokarin ganin ta cimma wannan buri nata bisa irin alkawurran da ta daukawa jama'ar kasar.

Game da sha'anin bunkasa sufuri ta ruwa kuwa, ministan ya ce tuni gwamnatin kasar ta fara zawarci masu zuba jari a wannan fannin.

Ya kara da cewa, gwamnatin kasar ta sha alwashin tabbatar da bin dokar baiwa 'yan kasar kashi 60 cikin 100 da kuma kashi 40 cikin 100 na hannayen jarin ga masu zuba jari na kasashen waje.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China