Kwamitin sulhun ya shirya wannan tattaunawar ce bisa bukatar da Rasha ta gabatar. Kafin ta shiga dakin tattaunawar, madam Samantha Power ta gaya wa 'yan jarida cewa, bangaren Amurka ya dauka cewa, an jefa boma-bomai ne kan na'urorin kungiyar IS, bayan da bangaren Rasha ya sanar da cewa, kayayyakin da aka kai hari, kayayyakin dakarun gwamnatin Sham ne, sai dai kawancen sojojin dake karkashin kasar Amurka ya daina jefa boma-boman, yanzu bangaren Amurka yana binciken lamarin. Idan aka tabbatar da cewa, kayayyakin dakarun gwamnatin Sham ne aka kaiwa wannan hari, to, ana iya cewa, wannan wani kuskure ne. Kuma Amurka ba ta jefa boma-boman da ganga ba. Ta kuma ce, kasar Rasha ta gangan ta kira wannan taron tattaunawar gaggawa.
Bayan kammala taron, Mr. Vitaly Churkin, wakilin dindindin na kasar Rasha dake MDD ya gaya wa 'yan jarida cewa, kasar Rasha za ta zuba ido kan martanin kasar Amurka, tana kuma fatan Amurka za ta mai da hankali sosai kan yadda za a daidaita batun Sham a siyasance. (Sanusi Chen)