Kwamishinan 'yan sandan jihar Zanna Ibrahim ya shaidawa manema labarai cewa, a jiya Alhamis ne wata tawagar ceto mai kunshe da 'yan sanda 100 da 'yan banga 30 suka yi nasarar ceto basaraken a wani kungurumin daji dake kusa da wajen birnin da aka sace basaraken.
Sakamakon bincken 'yan sanda na wucin gadi ya bayyana cewa, wasu da ake zaton Fulani makiyaya ne suka sace basaraken ranar Laraba a kan hanyarsa ta zuwa garin Asaba, babban birnin jihar Delta.
Rahotanni na cewa, 'yan sanda sun yi musayar wuta da wadanda suka sace basaraken, kafin daga bisani su yi nasarar ceto shi.(Ibrahim)