Ministan lafiyar kasar Isaac Adewole, ya shaidawa manema labarai cewa, a ranar Litinin ne aka samu rahoton bullar cutar wadda bera ke bazata, bayan da ta halaka wani babban jami'in kiwon lafiya da wani mai kula da dakin ajiye gawawwaki a cibiyar lafiya ta tarayya da ke garin Abeokuta a jihar Ogun.
Ministan ya ce, yanzu haka an umarci cibiyar kare yaduwar cututtuka ta kasa, da ta gudanar da bincike da nufin dakatar da kuma hana yaduwar cutar.
Bayanai na nuna cewa, ana kamuwa da cutar ce idan yawu, ko fitsari, da najasan bere ya shiga abinci ko ruwa kuma mutane suka yi amfani da shi bisa kuskure. A wasu lokutan alamomin cutar sun yi kama da na zazzabin cizon saura ko malariya. A dai magance cutar da zarar an gano ta a kan lokaci. (Ibrahim)