in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wani jirgin saman Rasha ya fada teku
2016-12-26 09:31:12 cri
A Jiya Lahadi, 25 ga wata ne, rahoto daga ma'aikatar tsaron kasar Rasha ya ce, wani jirgin saman soja, samfurin Tu-154, wanda ke kan hanyarsa ta zuwa kasar Siriya daga birnin Sochi, ya fada tekun Black Sea,inda dukkan fasinjoji 84 da ma'aikata 8 dake cikin jirgin suka rasa rayukansu.

Kafofin watsa labaran kasar Rasha sun ce, daga cikin fasinjojin 84, akwai 'yan wasa 64 na shahararriyar kungiyar wasan kade-kade da raye-raye ta sojan Rasha, mai suna Alexandrov Ensemble, wadanda ke kan hanyarsu ta zuwa sansanin sojan saman Hmeymim na kasar Rasha dake kasar Siriya, don gabatar da wasannin murnar sabuwar shekara.

Daga cikin fasinjojin kuma, akwai shugaban sashin kula da al'adu na ma'aikatar tsaron Rasha, da babban jagoran kungiyar wasan kide-kide ta rundunar sojan Rasha, tare kuma da 'yan jaridun kasar guda 9.

A wani labarin kuma, shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya sanar da yau Litinin 26 ga wata, a matsayin ranar zaman makoki.

Haka kuma, ya ba da umurnin binciken musabbabin aukuwar hatsarin. (Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China