Dmitri Peskov ya ce, kasarsa za ta tsara matakai bisa umurnin shugaba Vladimir Putin, domin mai da martani kan takunkumin da Amurka ta sanya mata.
A cewarsa, wannan takunkumin da Barack Obama ya sanyawa Rasha, zai lalata dangantakar dake tsakanin Rasha da Amurka, kana ya kawo illa ga manufar diflomasiyya da zababben shugaban kasar wato Donald Trump, ya tsara.
Peskov ya kuma ce, gwamnatin Obama na kokarin matsawa gwamnatin Trump lamba ta hanyar nuna kiyayya ga kasar ta Rasha.
Mista Peskov ya kara da cewa, gwamnatin Rasha tana fatan gwamnatin Obama za ta gyara matakanta, ta yadda huldar dake tsakanin kasashen biyu za ta bunkasa ta hanyar da ta dace.
Jiya Alhamis 29 ga wata, shugaban kasar Amurka mai barin gado Barack Obama ya sanar da cewa, kasarsa za ta sanyawa Rasha takunkumi, bisa zarginta da yin katsalandan cikin harkokin zaben Amurka ta yanar gizo wato Intanet.
Har ila yau, a jiya Alhamis din ne, ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta sanar da korar 'yan diflomasiyyar Rasha 35 daga kasar. (Murtala Zhang)