in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Fitch: Babu baraza game gibin tattalin arziki a kasar Sin
2016-12-07 11:09:21 cri
Hukumar kididdiga ta Fitch ta bayyana cikin rahotonta na baya bayan nan cewa, duk da irin matsaloli na koma bayan da ake fuskanta a duniya, kasar Sin tana da isassun hanyoyin bunkasa tattalin arzikinta ba tare da fuskantar wasu sauye-sauye game da sha'anin tsarin tattalin arzikin kasar ba.

A rahoton da Fitch ta fitar a jiya Talata ta nuna cewa, duk wata tangardar tattalin arziki da za ta iya shafar kasar Sin, dole ne zai haifar da nakasu ga shiyyar nahiyar Asiya baki daya, kuma lamarin zai iya rage darajar kudin yuan na kasar Sin.

Fitch ta ce "mun yi amanna cewa kasar Sin tana da dabarun mulki da kuma karfin tattalin arzikin da za ta iya shawo kan duk wata matsala da ta shafi cike da gibin tattalin arziki, ko da yake wannan damar za ta iya gamuwa da cikas muddin ba'a dauki matakan da suka dace a kan lokaci ba."

Fitch ta ce tana tsammanin yanayin karfin tattalin arziki a nahiyar Asiya zai samu bunkasuwa, duk da kasancewar karuwar harkokin cinikayya a nahiyar ta Asiya yana fuskantar tafiyar hawainiya sakamon ja da bayan da harkokin kasuwannin duniya ke fuskanta a halin yanzu.

Hasashen Fitch game da karuwar GDP a shekarar 2017, ya nuna yiwuwar samun karin kasuwanni 11 a Asiya da suka hada da kasar Sin, Indiya da kuma Vietnam, zai kai kashi 5.5 cikin dari, sama da sauran sassa na duniya. (Ahmad)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China