in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Zimbabwe ta fitar da giwaye zuwa kasar Sin ba domin biyan bashi ba
2016-12-29 13:58:43 cri
Wasu kafofin watsa labaran ketare sun bayyana cewa, uwargidan shugaban kasar Zimbabwe Grace Mugabe ta baiwa wani gidan naman daji na kasar Sin wasu namun daji, cikin har da 'yayan giwaye guda 35, zakoki guda 8, kuraye guda 12 da kuma rakumin dawa guda daya, a madadin kudin takalman da rigunan sojoji da kasar ta saya.

Sai dai wani dan kasar Sin da ya sa hannun batun ya bayyana cewa, wannan labarin ba gaskiya ba ne.

Dangane da wannan batu, Madam Song Li wadda ta kafa asusun kare namun daji tsakanin kasar Sin da kasar Zimbabwe ta bayyana cewa, wadannan giwaye 35 namun daji da gidajen namun dajin Shanghai da na Beijing da gidan namun dajin Hangzhou suka saya ne daga kasar Zimbabwe, masu cinikin dabbobi na kasar Sin da hukumar kula da harkokin lambun shan iska na kasar Zimbabwe sun kuma kulla yarjejeniya kan wannan ciniki a hukunce.

Sa'an nan, wandannan gidajen naman daji sun biya hukumar kula da namun daji ta kasar Zimbabwe da kuma lambun shan iska na Zimbabwe kudi kai tsaye.

Bugu da kari, wadannan gidajen namun daji na kasar Sin sun sayi giwaye guda 35 ne daga kasar Zimbabwe, ba kamar yadda kafofin watsa labarai na kasashen ketare suke yayatawa, wai an baiwa kasar Sin 'ya'yan giwaye guda 35, zakoki guda 8, kuraye guda 12 da kuma rakumin dawa guda daya ba. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China