A yayin ganawar, Zhang Dejiang ya ce, akwai zumunci sosai tsakanin kasashen Sin da Zimbabwe matakin da ya ba da tabbacin aza harsashin bunkasuwar dangantakar dake tsakanin kasashen biyu a siyasance.
Zhang ya kara da cewa, a shekarar da ta wuce, shugaba Xi Jinping na kasar Sin da takwaransa na Zimbabwe Robert Mugabe sun tsara shirin bunkasa dangantakar dake tsakanin kasashensu a nan gaba, don haka kamata ya yi bangarorin biyu su yi kokarin ganin wannan ra'ayi da shugabannin biyu suka cimma ya tabbata. Kaza lika Zhang ya ce, majalisar wakilan jama'ar Sin tana son karfafa dangantakar abokantaka tsakaninta da majalisun dattawa da ta wakilai na kasar Zimbabwe.
A nasa bangaren, Edna Madzongwe ya ce, kasar Zimbabwe na mayar da hankali kan dangantakar abokantaka dake tsakaninta da Sin, tana kuma fatan karfafa yin cudanya da hadin kai tsakanin hukumomin kafa dokoki na kasashen biyu ta wannan ziyarar, da nufin bunkasa hadin kai a fannoni daban daban. (Bilkisu)