A yayin ganawar, Yu ya ce, dangantakar dake tsakanin Sin da Zimbabwe abin koyi ne wajen hadin kai tsakanin Sin da kasashen Afirka. Ya kara da cewa, Sin na mayar da hankali sosai kan dangantakar abokantaka dake tsakanin kasashen biyu, tana kuma fatan bangarorin biyu za su yi kokarin tabbatar da ra'ayoyin da shugabanninsu suka cimma.
A nasa bangaren Madzongwe ya bayyana cewa, majalisar dattawan kasar Zimbabwe na son karfafa hadin kai da cudanya tare da majalisar ba da shawara kan harkokin siyasan kasar Sin, don ciyar da dangantakar dake tsakanin kasashen biyu gaba. (Bilkisu)