Dajin na Sambisa dake da nisan kilomita sittin a kudu maso gabashin Maidugurin Jihar Borno, ya yi kaurin suna a matsayin wani sansanin bada horo na kungiyar.
Tukur Buratai, ya shaidawa mahalarta wani taro da aka yi a Abuja babban birnin kasar cewa, dakarun na samun nasara a aikin da suke a dajin.
A cewar babban hafsan, rundunar sojin Nijeria ta shiga dajin ne bisa shawarar da ta yanke, na jajircewa ta kowanne bangare wajen dakile ayyukan tsageru da 'yan ta'adda, da nufin tabbatar da zaman lafiya a kasar.
Ya kuma dora nasarar da rundunar ke samu a ayyukan da take a yankin arewa maso gabashin da sauran sassan kasar, akan irin goyon baya da take samu daga shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Yankin arewa maso gabashin Nijeriya dai, ya kasance tungar 'yan tada kayar baya na Boko Haram cikin shekaru shida da suka gabata, inda ya yi ta fuskantar hare-hare daban-daban.(Fa'iza)