in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sama da mutane miliyan 3 ne rikici ya raba da matsugunansu a gabar tafkin Chadi
2016-12-10 12:54:33 cri

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta kasa da kasa wato IOM ta sanar cewa, rikicin Boko Haram ya raba sama da mutane miliyan 3 da dubu 600 daga gidajensu a yankin gabatar tafkin Chadi daga shekarar 2009, kuma daga cikin adadin har yanzu mutane sama da miliyan 2 da dubu 600 ba su sake komawa garuruwansu ba tun bayan da tashin hankalin ya daidaita su.

Daraktan shiyyar yammaci da tsakiyar Afrika Richard Danziger, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa, ya ce akwai matukar bukatar kai agaji a yankunan, kasancewa al'ummar na cikin mawuyacin hali dake bukatar a kai musu daukin gaggawa.

Ya kara da cewa, akwai bukatar hukumomi su hada gwiwa da sauran kungiyoyin ba da agaji na kasa da kasa domin hanzarta samar da muhimman abubuwan da mutanen da rikicin ya shafa suke matukar bukata.

Ya ce a halin yanzu, kashi 82 cikin 100 na mutanen da rikicin ya daidaita suna zaune ne a Najeriya, sannan akwai kaso 9 dake zaune a Jamhuriyar Kamaru, kana kaso 6 na zaune a Nijer, yayin da kaso 3 da daga cikin mutanen na zaune ne a kasar Chadi.

A cewar IOM, kashi 93 cikin 100 na mutanen da rikicin ya tilastawa ficewa daga gidajensu suna zaune ne a kasashen su na asali, sannna kaso 7 daga cikinsu kuma suna neman mafaka a makwabtan kasashe.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China