in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dakarun Najeriya sun kubutar da mutane 800 daga hannun mayakan Boko Haram
2016-12-09 10:42:10 cri
Kimanin mutane 800 ne sojojin Najeriya suka kubutar daga hannun mayakan Boko Haram a jahar Borno dake shiyyar arewa maso gabashin kasar.

Lucky Irabor, shi ne kwamandan runduna ta musamman ta Lafiya Dole, ya shedawa taron manema labarai a Maiduguri babban birnin jahar Borno cewa, dakarun Najeriyar sun kubutar da mutanen ne a cigaba da farautar mayakan yan ta'adda dake shiyyar.

Yace sun ceto mutanen ne tun a ranar 23 ga watan Nuwamba.

Irabor, ya kara da cewa, a cigaba da sunturin da sojojin ke gudanarwa, sun samu nasarar damke wasu daga cikin mayakan na Boko Haram a lokacin da suke yunkurin tserewa daga maboyarsu a dajin Sambisa.

A ranar Lahadin data gabata ne, babban hafsan sojojin kasa na Najeriyar Tukur Buratai, ya umarci dakarun kasar dake aiki a shiyyar arewa maso gabashin kasar, dasu hanzarta kammala aikinsu na karshe na murkushe mayakan na Boko Haram.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China