A sanarwar da ofishin kula da kimiyyar binciken sararin samaniyar ta kasar Sin ya gabatar, ya ce an tura na'urar gwaje gwajen ne daga birnin Beijing tun a ranar Alhamis ta jirgin kasa, kuma ta isa cibiyar a jiya Asabar, kana wannan ya nuna cewar an zo mataki na gaba na fara aiwatar da shirin harba na'urorin binciken sararin samaniyar ta Tiangong-2 da Shenzhou-11.
Sanarwar ta kara da cewar, za'a fara harhada na'urar ne da kuma gwada ta a cibiyar, kafin daga bisani a harba na'urar wanda ake sa ran gudanarwa a watan Satumba. (Ahamd Fagam)