in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta harba tauraron dan Adama na sadarwa na farko domin wayar salula ta tafi da gidanka
2016-08-06 12:03:26 cri
Da wajen karfe 12 da minti 22 na sanyin safen Asabar, 6 ga wata ne, kasar Sin ta yi amfani da roka mai harba kaya kirar Long March B ta harba tauraron dan Adama na farko na Tiantong domin tsarin wayar salula, wannan ne karo na farko da kasar Sin ta harba tauraron dan Adama na sadarwa domin tsarin wayar salula musamman na tafi da gidanka.

Tsarin wayar salula na tafiya da gidanka na farko na Tiantong, tsari ne da kasar Sin ta dogora da kanta ta yi nazarinsa kuma ta kera shi, kuma wani muhimmin sashe ne ga ayyukan yau da kullum na sadarwa da kasar Sin take kafawa a sararin sama.

Bisa shirin da aka tsara, za a iya kafa wani tsarin sadarwa na tafi da gidanka bisa tsarin sadarwa na Tiantong dake sararin sama, da tsarin sadarwa na tafi da gidanka da aka kafa a doron duniyarmu, kuma za a iya ba da ingantaciyyar hidimar sadarwa ta wayar salula ta tafi da gidanka ga al'ummomin kasar Sin da yankunan dake kewayenta da wasu yankunan Gabas na tsakiya da na Afirka da yawancin yankunan teku dake tekun Pacifik da na Indiya a kowane lokaci cikin kowane irin yanayin duniya. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China